- PDP na son dawo da tsofin yayanta da iyayenta gida gabanin zaben badi
- Obasanjo baya so Atiku yayi shugaban kasa a tun fil-azal
- An gano cewa sun fara bin ta karkashin kasa don lallabarsa ya yafe wa yaron nasa
A yunkurin jam'iyyar PDP na ganin cewa ta dinke barakar da ke tsakanin yan jam'iyyar sakamakon ganin gabatowar zaben 2019, jam'iyyar ta fara dabarun jawo hankalin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo don ya dawo jam'iyyar a cikin satittika masu zuwa.
Majiyar mu tace bayan kwamitin hadin kai da kwamitin sulhu da ke ta kokarin tattaro tsofafin yan jam'iyyar, kwamitin shugabancin jam'iyyar karkashin Prince Uche Secondus sun kirkiro wata hanyar kaiwa ga Obasanjo, zababben shugaban kasa na farko a karkashin jam'iyyar ta PDP a 1999.
Kamar yanda majiyar tamu ta sanar damu, yunkurin na kaiwa ga shugaban Obasanjo ya hada da sanya Canal Habibu Shuaibu, tsohon shugaban mulkin soja na jihar Niger da filato don ya mika sakon neman sulhu ga shugaban amintattun jam'iyyar.
Majiyar tamu mai karfi tace Canal Shuaibu dai har yanzu na hannun dama ne ga tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da kuma Obasanjo. Canal din na da tabbacin shuwagabannin zasu yadda makaman da suka dauka na fada da jam'iyyar ta PDP.
DUBA WANNAN: Jiga-jigan APC na kacamiya kan kujerun takara a Abuja
Idan zamu iya tunawa, Kanal din kwanan nan aka nawa shi shugaban yakin neman zaben Kabiru Turaki na arewa kuma yana da murya babba gurin kiran hadin kan jam'iyyar PDP wanda yayi ba da dadewa ba a Abuja.
Wata majiyar mu da ta bukaci da kada a bayyana shi, yace daya daga cikin burin Shuaibu shine jam'iyyar tayi biyayya ga dokokin zaben Dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019.
"Lokacin da jam'iyyar tayi taron manema labarai a kwanaki don Kiran wadanda suka bar jam'iyyar dasu dawo, babban kira ne ga duk masoyan Najeriya kuma masu son suga cigaban Najeriya bayan karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019. Mun San cewa baba bai iya mulki ba kuma mun shirya gyara kurakuran mu na baya. Daga baya Baba zai tabbatar da cewa APC basu da dabarun mulki a don haka ne muke so ayi sulhu." inji Shuaibu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kHBtcGphYn9xfZhmmGaan66ybq3SoZxmqJSlerWtjJ%2BYq5ldrra4rYyomZqrkaO3sHnKoqmapqmaeqW7zWawmmWUlsSwecaim5pmmKm6rQ%3D%3D